Thursday, 21 July 2016

Kare yayi kalaci da jariri a Katsina..

vllkyt7djvn0p3uan.060fd38e
Jaridar Punch ta ruwaito cewa wadanda ake zargi da tafka laifin sun hada da budurwa yar shekara 15 mai suna Wasila Haruna, da kishiyar mamanta da uwar tata. Wasila itace ta haifin jaririn, sai dai ana zargin wani mutum ne mai suna Musa Garba yayi mata fyade, a dalilin haka ne dangin yarinyar suke ganin haihuwar jaririn ya zame masu abin kunya, tunda dai cikin shege ne. daga nan ne fa uwar wasila tare da kishiyarta suka yanke shawarar mika jaririn ga wani kare
don yayi kalaci das hi. Dakacin kauyen ne ya kai karar su zuwa ofishin yan’sanda, wanda yasa yasandan sukayi ram da dangin yarinyar da shi Musan da ake zarginsa da laifin yiwa yarinyar fyade. Dagan an kuma aka gurfanar dasu a gaban kuliya manta sabo aka laifuka guda uku da suka hada da laifin kisan kai, hadin baki akan aikata babban laifi da kuma fyade. Acewar lauya mai kara yace lafin da suka aikata ya ci karo da sashi na 235, 387, da kuma sashi na 85 na dokokin pinal. A yanzu haka ana tsare da Musa Garba da zargin aikata fyade. Alakalin kotun Nura Ladan ya baiwa yansanda umarnin su garkame mai lafin har sai ranar da za’a cigaba da shari’ar a ranar 8 ga watan agusat na shekara 2016. Shin mutanen nan zasu samu rahamar Allah kuwa?

No comments:

Post a Comment

DROP YOUR COMMENTS AND YOU STAND A CHANCE TO WIN OUR MONTHLY GIVEAWAY PRIZES...