Thursday 21 July 2016

Sunayen Buhari 5 da ‘yan Najeriya suka sa masa..

anti-corruption war
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na shan yabo da suka a wajen ‘yan kasar tun lokacin da ya karbi ragamar mulkin kasar a shekarar da ta wuce, dangane da hake ne ma ya sa wasu ‘yan kasar suka lakaba masa wasu sunaye don nuna jin dadinsu da kuma akasin hakan dangane da yaddda ya ke tafiyar da mulkin kasar, ga wasu daga cikin sunayen.

Shugaban ‘yan Arewa: Shugaba Buhari ya samu wannan suna ne a bisa yadda yawancin nade-naden da yayi a manyan mukamai duk daga arewacin kasar suke. Wanda hakan ya sa ‘yan kudanci suka ke kiransa da wannan suna.
Shagaban Canji : Ba kamar yadda a lokacin yakin neman zabe da shugaban ke ikirarin canji ba, a yanzu a cewar wasu na ganin cewa canjin ya gaza kai wa ga wasu muhimman batutuwan da suka shafi kasa.
Baba Yawale: wasu na kiran shugaban da wannan suna ne saboda yawan tafiye-tafiyen da shugaban ya rika yi zuwa kasashen waje. An dai ki kiyasta cewa shugaba Buhari ta fita kasashen waje sau 30 a shekara guda da kama mulkinsa, yayin da ya kai ziyara jihohi 5 kacal a kasar.
Baba go silo: Wasu na kiran shugaban da wannan suna ne saboda yadda ya ke tafi da mulkinsa wanda wasu ke ganin cewa ana daukar tsawon lokaci wajen aiwatar da wasu muhimman manufofi ko ayyuka.
Dan daura mai dala: Wasu na kiran shugaban ne da wannan suna saboda yadda Naira ke Dalar Amurka ke shan kasha a hannun Dalar Amurka a kasuwar canji.

No comments:

Post a Comment

DROP YOUR COMMENTS AND YOU STAND A CHANCE TO WIN OUR MONTHLY GIVEAWAY PRIZES...